Hukumar hana sha da fatauncin miyagun kwayoyi ta kasa(NDLEA) ta kai farmaki wani gida da aka shirya bikin shan miyagun kwayoyi a Osogbo a ranar Asabar.

Mai Magana da yawun hukumar NDLEA, Femi Babafemi, ne ya tabbatar da hakan a ranar Lahadi a Abuja inda ya ce Jami’an hukumar sun cafke wadanda suka shirya bikin shan kwayoyin tare da kama muggan kwayoyi.
Babafemi, ya ce jami’an hukumar sun kai farmakin ne bayan samun bayanan sirri na shirya taron wanda aka yiwa taken “Unholy Alliance for Stoners and Drunkards’’.
Ya kara da cewa dillalan kwayoyin suna safarar manyan kwayoyi daban-daban da kuma ta’ammuli dasu.
“Wadanda suka shirya taron na fara tattaruwa a yankin Berrymist Lounge dake unguwar Ofatedo a birnin Osogbo domin soma bikin ne jami’an NDLEA suka far musu.
“Mutanen da aka kama sun hada da Ikotu Omolayo mai shekara 25, Fola Olabode ‘dan shekara 30 da Akorede Adunni Ajibola mai shekaru 22. Tuni aka gayyaci hukumomin rukunin gidajen domin bincike,’’ acewar Babafemi.
Like
Dislike
Love
Angry
Sad
Funny
Wow
Majalisar Dinkin Duniya Ta Bukaci Rundunar Sojin Najeriya Da Ta Yi Kwaskwarima Ga Dokokinta
December 07, 2023Gwamnatin Saliyo ta kafa dokar hana fita bayan harin ‘yan bindiga kan rumbun adana makamai
November 27, 2023Tinubu ya nada Akinyelure shugaban NNPC,yayin da ya sake nada Kyari Shugaba
November 28, 2023Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Fara Kai Agaji Ga Iyalan Mutanen Da Harin Jirgin Sojin Najeriya Ya Hallaka
December 07, 2023
Comments 0