Hukumar Lafiya ta Duniya(WHO) ta tabbatar da cewa tsawon kwanaki hudu kenan ana gudanar da aikin rigakafin kamuwa da cutar mashako wato Diptheria a jihar Zinder ta jamhuriyyar Nijar.
Hukumar Lafiya ta Duniya(WHO) ta tabbatar da cewa tsawon kwanaki hudu kenan ana gudanar da aikin rigakafin kamuwa da cutar mashako wato Diptheria a jihar Zinder ta jamhuriyyar Nijar.
Hukumomin Lafiya a Nijar Sun Kaddamar Da Shirin Rigakafin Cutar Mashako
Hukumar Lafiya ta Duniya(WHO) ta tabbatar da cewa tsawon kwanaki hudu kenan ana gudanar da aikin rigakafin kamuwa da cutar mashako wato Diptheria a jihar Zinder ta jamhuriyyar Nijar.
Jihar Zinder dai ita ke zama cibiyar annobar cikin shekaru 20 a kasar.
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bayyana cewa tun a watan Yuli da cutar ta mashako ta barke a Nijar, zuwa yanzu fiye da mutane 200 daga cikin mutane dubu 2 da 936 da suka kamu da cutar ne suka mutu.
Hukumar WHO ta ce a ranar 20 ga watan Nuwambar 2023 ne, hukumomin lafiya a Nijar suka kaddamar da shirin rigakafin a Matameye ta Zinder wadda ke da kashi 48.7 na masu dauke da cutar ta Diptheria a kasar.
Akalla kananan yara dubu dari uku ne kama daga jarirai zuwa ‘yan shekara 14, aka yi wa rigakafin yayinda adadin jami’an kiwon lafiya dubu daya ke gudanar da aikin.
Cutar ta Diptheria dai na haifar zazzabi da ciwon kai da kumburin wuya da kuma yoyon hanci hadi da tari ga saurin yaduwa.
Like
Dislike
Love
Angry
Sad
Funny
Wow
Majalisar Dinkin Duniya Ta Bukaci Rundunar Sojin Najeriya Da Ta Yi Kwaskwarima Ga Dokokinta
December 07, 2023Gwamnatin Saliyo ta kafa dokar hana fita bayan harin ‘yan bindiga kan rumbun adana makamai
November 27, 2023Tinubu ya nada Akinyelure shugaban NNPC,yayin da ya sake nada Kyari Shugaba
November 28, 2023Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Fara Kai Agaji Ga Iyalan Mutanen Da Harin Jirgin Sojin Najeriya Ya Hallaka
December 07, 2023
Comments 0