Majalisar Dokokin Najeriya ta bayyana cewa ba za ta lamunci sakaci daga ma'aikatan hukumomin gwamnati ba, a yayin da suka zo kare kasafin kuɗin ma'aikatun su a gaban kwamitoci daban-daban na zauren majalisar.

Shugaban Kwamitin Kula da Kasafin Kudi a Majalisar Dattawa, Solomon Adeola Olamilekan, ya bayyana haka yayin da yake jawabi ga manema labarai, inda yake maida martani kan rashin zuwan wasu shugabanin hukumomi zauren Majalisar a lokacin da ake zaman kare kasafin kudin shekara 2024, kamar yadda doka ta tanada.
Olamilekan ya ce batun rabon kudi domin yi wa jama'a aiki muhimmin lamari ne a tsarin dimokaradiyya, saboda haka yana kira ga shugaban kamfanin mai na ƙasa NNPC da sauran manyan shugaban ma'aikatu da su bayyana a gaban kwamitin a ranar Alhamis.
Har ila yau ya kuma kara da cewa akwai wasu batutuwa na kudi har Naira tiriliyan 11 da shugaban kamfanin man fetur ɗin Mele Kolo Kyari zai yi bayani a kan su, domin ƴan ƙasar nan su san halin da ake ciki.
Like
Dislike
Love
Angry
Sad
Funny
Wow
Majalisar Dinkin Duniya Ta Bukaci Rundunar Sojin Najeriya Da Ta Yi Kwaskwarima Ga Dokokinta
December 07, 2023Gwamnatin Saliyo ta kafa dokar hana fita bayan harin ‘yan bindiga kan rumbun adana makamai
November 27, 2023Tinubu ya nada Akinyelure shugaban NNPC,yayin da ya sake nada Kyari Shugaba
November 28, 2023Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Fara Kai Agaji Ga Iyalan Mutanen Da Harin Jirgin Sojin Najeriya Ya Hallaka
December 07, 2023
Comments 0