Majalisar Ɗinkin Duniya ta buƙaci rundunar sojin Najeriya da ta sake yin nazari tare da yin duba ga dokokinta na yaƙi da matsalar tsaro, domin kauce wa afka wa mutanen da ba su ji ba basu gani ba a faɗin ƙasar.

Shugaban sashen yaɗa labarai na ofishin kare haƙƙin ɗan adam a ofishin Majalisar ɗinkin duniya, Seif Magango, ya buƙaci hakan, yayin da yake mai da martani bisa hari na kuskure da rundunar Soji ta kai kan taron masu Maulidi a tudun biri dake jihar Kaduna.
Magango yace majalisar dinkin duniya tana tir da wannan hari da aka kai akan jama'a, duba da cewa ba wannan ne karon farko da ake samun makamancin hakan ba a Najeriya.
Har ila yau Mista Magango yace Duk da cewa Rundunar Sojin ta ce kuskure ne, amma majalisar ɗinkin Duniya tana ƙara kira ga Gwamnatin Najeriya da ta yi duk mai yiwuwa wajen kare rayukan fararen hula da dukiyoyinsu a nan gaba.
Like
Dislike
Love
Angry
Sad
Funny
Wow
Majalisar Dinkin Duniya Ta Bukaci Rundunar Sojin Najeriya Da Ta Yi Kwaskwarima Ga Dokokinta
December 07, 2023Gwamnatin Saliyo ta kafa dokar hana fita bayan harin ‘yan bindiga kan rumbun adana makamai
November 27, 2023Tinubu ya nada Akinyelure shugaban NNPC,yayin da ya sake nada Kyari Shugaba
November 28, 2023Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Fara Kai Agaji Ga Iyalan Mutanen Da Harin Jirgin Sojin Najeriya Ya Hallaka
December 07, 2023
Comments 0