Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale ne, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya sanyawa hannu a ranar Litinin mai taken: ‘Shugaba Tinubu ya nada kwamitin gudanarwa na hukumar NNPC.

A ranar Litinin ne shugaban kasa Bola Tinubu, ya nada Pius Akinyelure a matsayin sabon shugaban hukumar kula da harkokin man fetur ta kasa (Nigerian National Petroleum Company Limited) da zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Disamba, 2023.
Hakan ya faru ne a yayin da ya sake nada shugaban kamfanin mai ci Mele Kyari na wani wa’adi daban.
Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale ne, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya sanyawa hannu a ranar Litinin mai taken: ‘Shugaba Tinubu ya nada kwamitin gudanarwa na hukumar NNPC.
Mambobin hukumar sun hada da Umar Ajiya a matsayin babban jami’in kudi sai Ledum Mitee da Musa Tumsa da Ghali Muhammad a matsayin daraktoci.
Sauran b sun hada da Farfesa Mustapha Aliyu da David Ogbodo da Ms. Eunice Thomas.
Bugu da kari, shugaba Tinubu ya amince da nadin manyan sakatarorin dindindin guda biyu.
Su ne Mista Okokon Udo, wanda shi ne babban sakatare a ma’aikatar kudi ta tarayya, da kuma Gabriel Aduda, wanda yanzu ya zama babban sakataren ma’aikatar albarkatun man fetur ta tarayya.
Ya umarci dukkan wadanda aka nada da su aiwatar da manufofin makamashi dan samar da kudi daga albarkatun mai da iskar gas da Najeriya ke da su tare da ba da damar samar da sabbin hanyoyin samar da makamashi mai tsafta.
Like
Dislike
Love
Angry
Sad
Funny
Wow
Majalisar Dinkin Duniya Ta Bukaci Rundunar Sojin Najeriya Da Ta Yi Kwaskwarima Ga Dokokinta
December 07, 2023Gwamnatin Saliyo ta kafa dokar hana fita bayan harin ‘yan bindiga kan rumbun adana makamai
November 27, 2023Tinubu ya nada Akinyelure shugaban NNPC,yayin da ya sake nada Kyari Shugaba
November 28, 2023Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Fara Kai Agaji Ga Iyalan Mutanen Da Harin Jirgin Sojin Najeriya Ya Hallaka
December 07, 2023
Comments 0