Hukumar lafiya ta duniya(WHO) ta koka gameda karuwar masu kamuwa da cutar tarin Fuka a fadin jihar Born
Hukumar lafiya ta duniya(WHO) ta koka gameda karuwar masu kamuwa da cutar tarin Fuka a fadin jihar Born
Hukumar lafiya ta duniya(WHO) ta koka gameda karuwar masu kamuwa da cutar tarin Fuka a fadin jihar Borno.
Wakilin hukumar a Najeriya, Dr Walter Mulombo, ne ya bayyana hakan a lokacin taron hadin gwiwa kan lamurra da suka shafi yankin arewa maso gabashin Najeriya na WHO karo na 13 wanda ya gudana a Yola.
Kamfanin Dillancin labarai na Najeriya( NAN) ya ruwaito cewa tattaunawar ta shafi jihohin Borno da Adamawa da Yobe, wandanda rikicin mayakan Boko Haram ya shafa.
Sai dai, daraktan hukumar a Najeriya ya ce a shirye suke wajen aiki da gwamnatin Borno domin magance cutar.
Mulombo ya ce karuwar cutar a jihar na nufin zata iya zama wata annnoba a Najeriya baki daya muddin ba’a dauki mataki ba.
Don haka, Mulombo, ya bukaci masu ruwa da tsaki da su hada hannu domin cimma muradun karni na majalisar dinkin duniya.
Tunda farko dai Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya koka da cewa akalla kaso 50 na cibiyoyin lafiya ne aka yi asara a jihar da kuma ma’aikatan lafiya wadanda aka sace ko kashe su sakamakon rashin tsaro.
Like
Dislike
Love
Angry
Sad
Funny
Wow
Majalisar Dinkin Duniya Ta Bukaci Rundunar Sojin Najeriya Da Ta Yi Kwaskwarima Ga Dokokinta
December 07, 2023Gwamnatin Saliyo ta kafa dokar hana fita bayan harin ‘yan bindiga kan rumbun adana makamai
November 27, 2023Tinubu ya nada Akinyelure shugaban NNPC,yayin da ya sake nada Kyari Shugaba
November 28, 2023Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Fara Kai Agaji Ga Iyalan Mutanen Da Harin Jirgin Sojin Najeriya Ya Hallaka
December 07, 2023
Comments 0