Gwamnatin jihar Kaduna ta ce zuwa yanzu, ta fara kai kayayyakin agajin gaggawa ga iyalan mutanen da harin jirgin sojin Najeriya mara mutuƙi ya kai a kan taron masu maulidi a yankin Tudun biri dake ƙaramar hukumar igabi a jihar.

Babbar Sakataren hukumar bada Agajin gaggawa na jihar kaduna wato SEMA, Dokta Usaman Hayatu Mazadu ya bayyana haka, inda yace wannan yana daga cikin matakan da gwamnatin jihar ke ɗauka na tallafawa iyalan mutanen da lamarin ya ritsa dasu domin rage musu halin raɗaɗin da suke ciki.
Daga cikin kayayyakin tallafin da gwamnatin jihar kaduna ta bayar, wadda shine kashi na farko sun haɗa da Tufafi da kayan Abinci da Katifu da barguna da sauran su.
Har ila yau gwamnatin ta jaddada cewa ana cigaba da gudanar da bincike kan lamarin domin sake afkuwar hakan anan gaba, tare da alƙawarin ɗaukar nauyin mutanen da suka samu raunuka bayan faruwar iftila'in.
Like
Dislike
Love
Angry
Sad
Funny
Wow
Majalisar Dinkin Duniya Ta Bukaci Rundunar Sojin Najeriya Da Ta Yi Kwaskwarima Ga Dokokinta
December 07, 2023Gwamnatin Saliyo ta kafa dokar hana fita bayan harin ‘yan bindiga kan rumbun adana makamai
November 27, 2023Tinubu ya nada Akinyelure shugaban NNPC,yayin da ya sake nada Kyari Shugaba
November 28, 2023Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Fara Kai Agaji Ga Iyalan Mutanen Da Harin Jirgin Sojin Najeriya Ya Hallaka
December 07, 2023
Comments 0